Connect with us

News

Yadda gini mai hawa bakwai ya rufta a Legas

Published

on

 

Wani gini mai hawa bakwai da ake ginawa ya rufta a yankin Banana Island da ke Ikoyi a jihar Legas.

 

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ginin ya ruguje ne dazu da rana.

Za A Fara Ba Duk Matar Da Ta Haihu Miliyan 5 A Koriya Ta Kudu

A cewar kafar yaɗa labaran, ginin ya rufta a daidai lokacin da wasu daga cikin masu aikin ginin suka tashi.

 

Advertisement

Sai dai akwai wasu da rahotanni suka ce sun jikkata sakamakon lamarin.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Amodu Shakiri ya tabbatar da faruwar al’amarin.

 

Ya ce “mun samu kiran gaggawa da kusan ƙarfe 3:58pm. Muna ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wani da ya maƙale a ɓuraguzon ginin.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending