News
Tirela Ta Kashe Yaro A Wurin Dibar ‘Ganima’ A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani yaro ya rasu a yayin da wasu suka jikkata a wajen kwasar ‘ganima’ a gine-ginen da Gwamnatin Jihar Kano ta yi rusau a Filin Idi.
Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya faru ne yayin da matasa suka yi wa wani gini kawanya domin kwasar dibar karafunan rodi da kofofi ne wata babbar mota ta take yaron.
Wani Ganau ya ce “Muna tsaye a nan lokacin da yaron da wasu suka fito da kwano na rufi da wasu kofofi da rodi.
“Ba mu san wa ya biyo su ba. Suna da yawa amma yaron da ya yi rashin sa’a yana fitowa wata tirela ta take shi kuma nan take ya rasu.”
jaridar aminiya ta rawaito cewar ana fargabar wani ma ya rasu yayin da suke tsaka da dibar ‘ganima’ gini ya rufta musu.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya ce sun cafke mutum 49 da ke satar dukiyar al’umma da sunan ganima, a irin wadannan gine-gine da aka rushe.
Ya ce: “Wasu daga cikin kayan da muka kawo sun hada manyan kof
