News
Hukumar ICPC Ta Fara Gwanjon Kadarorin Data Kwace Daga Masu Karbar Rashawa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar yaki da cin hanci da kuma karbar rashawa ta kasa ICPC, Ta bude baje kolin gwanjojin kayayyakin da aka kama a bana, wanda aka mallakawa gwamnatin taraiyya su.
Mai magana da yawun hukumar uwargida, Azuka Oguguwa ce ta baiyana haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin a Abuja.
Makarantu Masu Zaman Kansu Zasu Kara Kudin Makaranta Saboda Janye Tallafin Mai
Ta Ambato shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owasanaye na alkawarin cewar za’a gudanar da aikin a faiyace batare da wata ‘kunbiya-‘kunbiya ba.
Daga nan sai ya yabawa masu sayen gwanjon kayayyakin saboda hadin kan da suke bawa hukumar, ya kuma sake basu tabbacin cewar za’a yi baje kolin a bude batare da wani ‘boye boye ba.
Advertisements
