Connect with us

News

Wasu da ake zargin Yan bindiga ne sun kashe mahaifin shugaban matasan Ohaneze Ndigbo

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Wasu da ake zargin Yan bindiga ne sun kashe mahaifin shugaban matasan Ohaneze Ndigbo, Aja Okeafor, a gonarsa da ke jihar Ebonyi.

CBN Ya Dage Takunkumin Daya Sanyawa Asusun Masu Ajiyar Kudin Waje

Wadanda ake zargin dai sun gudu ne zuwa wani daji da ke kusa da hanyar Ishiagu zuwa Mpu bayan sun kashe ma’aikacin INEC tare da yin garkuwa da matarsa.

Advertisement

Jaridar Daily post ta rawaito cewa  Demian Okeafor, shugaban matasan Ohaneze Ndigbo ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ta wayar tarho a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Ya ce, “Ina gida bayan hidimar coci sai aka kira ni aka kira ni cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mahaifina. Na yi ƙoƙari na garzaya wurin amma na kasa yin sa cikin lokaci. Daga baya, na je ofishin ’yan sanda tare da kanena, wanda tuni yana wurin, kuma aka tabbatar da hakan.”

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending