News
Wasu da ake zargin Yan bindiga ne sun kashe mahaifin shugaban matasan Ohaneze Ndigbo
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wasu da ake zargin Yan bindiga ne sun kashe mahaifin shugaban matasan Ohaneze Ndigbo, Aja Okeafor, a gonarsa da ke jihar Ebonyi.
CBN Ya Dage Takunkumin Daya Sanyawa Asusun Masu Ajiyar Kudin Waje
Wadanda ake zargin dai sun gudu ne zuwa wani daji da ke kusa da hanyar Ishiagu zuwa Mpu bayan sun kashe ma’aikacin INEC tare da yin garkuwa da matarsa.
Jaridar Daily post ta rawaito cewa Demian Okeafor, shugaban matasan Ohaneze Ndigbo ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ta wayar tarho a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
Ya ce, “Ina gida bayan hidimar coci sai aka kira ni aka kira ni cewa wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mahaifina. Na yi ƙoƙari na garzaya wurin amma na kasa yin sa cikin lokaci. Daga baya, na je ofishin ’yan sanda tare da kanena, wanda tuni yana wurin, kuma aka tabbatar da hakan.”
