Connect with us

Entertainment

Tattaunawar jaruma Hadiza Gabon ta janyo cece-kuce

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Ana cigaba da cece-kuce a dandalin sada zumunta, akan batun tattaunawar da jarumar masana’antar shirya finafinan  Kannywood, Hadiza Gabon, ke gudanarwa a shafin YouTube.

Anda take  gayyato abokan sana’ar ta, tare da yi musu tambayoyi masu zafi, wadanda wasu ganin tambayoyin sun fita daga kwarewar aikin jarida, don kuwa akwai wata jaruma da har sai da ta zubda hawaye a dalilin tambayoyin nata.

Advertisement

 

Babbar magana: waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da daurin aure a Kano.

Hadiza Gabon ta sanyawa shirin ta suna “Gabon’s Room Talk Show” wanda a baya bayan nan ta tattauna da mawaƙi El-Mu’az, tayi masa tambaya akan alaƙarsa da wata abokiyar sana’arsu, lamarin da ya fusata mawaƙin, har shima ya jefa mata wasu tambaya akan sana’ar da ta keyi da kuma yadda take samun kuɗi.

Advertisement

Marubuta a shafin Facebook na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu akan batun, inda mafi yawa ke sukar tsarin da jaruma Hadiza Gabon ke bi wajen yin tambayoyi ga baƙin ta, harma wasu na ganin ya kamata ta nemo kwarewar aikin jarida, domin tattaunawar ba iya ita kadai da baƙin ta ke gani ba, Duniya ce ke kallon su.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending