Connect with us

News

Ministan tsaron Rasha ya bayyana a Talabijin a karon farko bayan boren Wagner

Published

on

DAGA  KABIRU BASIRU BASIRU FULATAN

 

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu ya ziyarci sojojin kasar da ke yaki a Ukraine, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar RIA ya sanar a ranar Litinin din nan.

Wannan ne dai karo na farko da aka ga ministan a kafar talabijin tun bayan hatsaniyar da aka samu tsakanin sojojin Rasha na kuma na hanan Wagner.

Hankali Ya Koma Kan Nada Sabbin ‘Yan Majalisar Zartarwa Da Tinubu Zai Nada

Shoigu, wanda shugaban sojojin Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi kakkausar suka akan sa, ya gudanar da taro da daya daga cikin kwamandajin sojojin Rasha a Ukraine, kamar yadda hotunan da aka wallafa suka nuna.

A cewar wata sanarwar da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, ta ce ya yin taron ministan ya bayyana cewa babban nasara ne ganowa tare da lalata tsarin makaman Ukraine da sojojinta.

Advertisement

Hotunan sun nuna Shoigu ya na sauraron rahoton da aka gabatar masa kan halin da sojojin ke ciki a yankin, sannan ya hau jirgi mai saukar ungulu don gudanar da rangadi a wasu wuraren da Rasha ke riki da su.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending