News
Gwamnatin Jahar Katsina Zata Dauki Matasa 2400 Aiki Don Magance Matsalar Tsaro A Jahar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Katsina ta fara wani shiri na musamman don daukar matasa 2,400 domin magance matsalolin tsaro dake addabar wasu sassan jihar
Bayan dauka da ba matasan horo, za su hadu da jami’an tsaro domin kara samar da tsaro a kananan hukumomi 8 da suka sha fama da matsalolin tsaro a jihar
Irin Ministocin Da ‘Yan Nijeriya Ke Tsammani Daga Gwamnatin Tinubu.
A ranar Juma’ar nan 7th Juli, 2023 ne dai mataimakin Gwamnan jihar Hon Faruq Lawal Jobe ya kaddamar da rarraba takardun cikewa na ‘form’ ga shugabannin kananan hukumomin da lamarin ya shafa
Gwamnatin jihar dai ta ce babban makasudin wannan yunkuri, shi ne don karin maganar nan ta Hausawa dake cewa “da dan gari, a kan ci gari
Wadannan matasa sun san lungu da sako na yankunansu, don haka za su tallafi jami’an tsaro wajen bi kokuwa-kokuwa don fatattakar masu aikata assha a cikin al’umma
Idan dai zaku iya tunawa, lokacin yakin neman zabe, Malam Dikko Umaru Radda ya yi alkawarin cewa tsaro na a sahun gaba a cikin alkawurran da ya daukar wa al’ummar jihar
Inda ya buga misali da zuwa har wuraren da ake ganin ba su shiguwa ta dalilin ayyukan ‘yan bindiga a lokacin yakin neman zabe
A lokacin rarraba wadannan takardun cikewa na ‘form’, mataimakin Gwamnan jihar Katsina Hon Faruq Lawal Jobe ya ce
Sanin kowane cewa Mai Girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta’addanci musamman ma a kananan hukumomin da lamarin ya yi kamari
Mataimakin Gwamnan ya ce an shirya daukar wadannan matasa, su hadu da jami’an tsaro su ba su horo na musamman domin su tallafi jami’an tsaron wajen samar da tsaro
Hon Faruq Lawal Jobe ya ce za a dauki matasa 300 a kowace karamar hukuma 8 da lamarin ya fi kamari. Sannan ya ce za a dauki matasan da ba su wuce shekaru 35 da haihuwa ba kuma masu tarihin ladabi da biyayya a cikin al’umma
Ya bukaci jagororin kananan hukumomin da su saka tsoron Allah wajen zaben mutane nagari kuma masu kishin dake son tsare rayuka da dukiyoyin al’ummominsu don a cimma nasara
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Arch. Ahmad Musa Dangiwa ya ce kwanaki kalilan da suka shude, gwamnatin jihar ta gana da shugabannin kananan hukumomi, inda aka tattauna sosai
