Connect with us

News

Rundunar Sojoji sun ceto ƙarin mata biyar daga hannun ‘yan fashi a Zamfara

Published

on

Sojojin najeriya

DAGA KABIRU BASIRU

Jami’an tsaro a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce sun ceto ƙarin mutum biyar daga hannun ‘yan fashin daji a yau Asabar bayan an yi garkuwa da su.

Kwamandan Rundunar Hadarin Daji Janar Sani Ahmed ne ya tabbatar wa da manema labarai kuɓutar mutanen waɗanda dukkansu mata ne.

Advertisement

Gwamnatin Jahar Katsina Zata Dauki Matasa 2400 Aiki Don Magance Matsalar Tsaro A Jahar

An ceto su ne a Ƙaramar Hukumar Maru da ke jihar ta Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Rahotanni na nuni da cewa Adadin ƙari ne a kan sama da mutum 60 da rundunar ta ce ta ceto a farmakin da ta kaddamar kan ‘yan fashin dajin daga jihar Kebbi mai maƙwabtaka zuwa Zamfara cikin kwana tara da suka gabata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending