Connect with us

News

Gaskiyar abinda ya faru game da matar da ta kashe mijinta a, jihar Bauchi.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Rundunar ‘Yan-sanda a jihar Bauchi, ta tabbatar da labarin kisan gillar da wata matashiyar matar aure mai suna Maimunatu tayi wa mijinta mai suna Aliyu Mohammad.

Advertisement

Maimunatu Sulaiman ‘yar shekara 21 mazauniyar unguwar Kofar-Dumi dake cikin garin Bauchi ta kashe mijinta, Aliyu Muhammad sakamakon rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu.

Rundunar Sojoji sun ceto ƙarin mata biyar daga hannun ‘yan fashi a Zamfara

Wata majiya daga unguwar ta bayyana cewa, an samu rashin jituwa ne a tsakanin miji da matar sakamakon yunkurin da mijin ya yi na kara aure.

Advertisement

A wata ruwayar kuma, ance mijin nata yana mata fada ne kan yawan fita yawo da take yi.!

Bayan samun husuma cikin dare tsakanin su, sai Maimuna ta dauki wuka ta daddaba wa mijin nata, a kirjinsa da gefen cikin sa, wanda hakan ya yi sanadiyar ajalinsa.

Advertisement

Hakan ya faru ne a ranar 5 ga watan Yulin 2023 a unguwar Kofar-Dumi. Bayanai sun ce ana kyautata zaton ma wukar ma ta karbi aron ta ne!

Jaridar Nigerian journal ta rawaito cewa Yanzu haka dai Rundunar ‘yan-sandan jihar Bauchi ta ce, ta cafke matar da ake zargi da kisan kan.

Advertisement

A sanarwa da kakakin ‘yan-sandan jihar, Bauchi ASP Aminu Gimba Ahmed ya fitar a ranar Juma’a, ta ce, “A ranar 5 ga watan Yuli 2023 jami’an caji ofis din ‘yansanda da ke Township, Bauchi sun kama wata Maimunatu Sulaiman kan zargin aikata kisan kai.

“Lokacin da jami’an suka samu rahoton faruwar lamarin, sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru tare da daukar wanda lamarin ya ratsu da shi da ita kanta wadda ake zargi zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Advertisement

“Amma likitoci sun tabbatar da mutuwar mijin sakamakon rauni da ya samu a kirjinsa, yayin da ita kuma wadda ake zargin ta samu wasu raunuka a cikinta.” da ake zargin ta yanka kanta ne domin bat da sawu da za’a iya zaton hari aka kai musu duka.

Binciken ‘yansanda ya nuna cewa wadda ake zargin ta soki mijinta a kirjinsa sakamakon rashin jituwar da ta barke a tsakaninsu.

Advertisement

Wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Auwal Musa Mohammad, ya umarci mayar da binciken lamarin zuwa sashen kula da manyan laifuka (SCID) don zurfafa bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending