News
An Samu Raguwar Hatsarin Mota da ake fuskanta a yayin Babbar Sallar bana.– FRSC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta ce an samu raguwar yawan hatsarin motar da ake fuskanta a yayin Babbar Sallar bana.
Hukumar ta kuma ce hakan na nufin an samu rangwame hatta a yawan hatsarin da kuma adadin wadanda ke mutuwa ko jin rauni idan aka yi hatsari.
Shugaba Tinubu Na Son Majalisa Ta Sahale Masa Kashe Biliyan 500 Na Rage Radadin Cire Tallafi
Hukumar ta ce yayin bukukuwan da aka kammala a kwanan nan, yawan haduran sun ragu da kimanin kaso 25 cikin 100, sai jin rauni da kaso 43, yayin da mace-mace ya ragu da kaso 53.
A cikin watan sanarwa da Kakakin hukumar na kasa, Bisi Kazeem ya fitar ranar Laraba, ya alakanta nasarar da sabon salon da hukumarsu ta dauka wajen wayar da kan masu tuki.
A cewar sanarwar, sabanin mutum 88 da suka mutu da 373 da suka jikkata a Babbar Sallar bara, a bana mutum 38 ne suka rasu, 211 kuma suka jikkata.
Ya kuma ce hukumar ta tattara yawan laifukan da aka aikata da suka kai 4,682 a hanyoyi 2,053 a tsakanin lokacin.
