News
Babban bankin kasa CBN ya kara kudin ruwa daga kashi 18.5 zuwa kashi 18.75 cikin dari.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Babban bankin kasa CBN ya kara kudin ruwa daga kashi 18.5 zuwa kashi 18.75 cikin dari.
Mukaddashin gwamnan babban bankin kasa CBN, Folashodun Shonubi ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan taron kwamitin kula da harkokin kudi na bankin a Abuja.
Wannan shi ne mataki na farko da kwamitin kudi ya yanke tun bayan hawan Shugaban kasa Bola Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Mukaddashin gwamnan babban bankin kasar ya ce kara kudin ruwan ya taka rawar gani wajen samun matsakaicin hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.
Advertisements
