News
Tinubu ya nada Atiku Bagudu, Bello Matawalle, Simon Lalong da karin mutum 16 ministoci
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike wa da majalisar dattawan kasar sunayen tsoffin gwamnonin jihar Kebbi, Zamfara, Filato da Yobe domin ya nada su a mukaman ministoci.
Shugaban majalisar dattawan kasar nan Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a zaman majalisar na yau Laraba.
Tsoffin gwamnonin na cikin karin mutum 19 da Shugaba Tinubu ya aike da sunayensu domin a tabbatar da su a mukamin ministoci.
Tsoffin gwamnonin su ne Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Bello Matawalle na jihar Zamfara, Simon Lalong na jihar Filato da Ibrahim Giedam na jihar Yobe.
Sauran su ne: Ahmed Tijjani Gwarzo Maryam Shetti Dr Tunji Alausa Yusuf Tanko Sununu, Shua’ibu Abubakar Audu Senator Aliyu Sahabi Abdulahi Senata Henekin Lokpobiri Zaphaniah Jisalo
