Connect with us

News

Hukumar Korota ta Haramtawa Jami,an ta amfani da Gora Akan Tituna.

Published

on

Shugaban hukumar Karota Faisal Mahmud Kabir

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

 

Advertisement

Shugaban hukumar Karota Faisal Mahmud Kabir ya ce daga cikin nau’in horon sanin makamar aiki da ake bawa jami’an za su iya gudanar da aikin su ba tare da amfani da Gora ba

A cewarsa yin amfani da Gora ya saɓa da dokar da ta kafa Hukumar ta KAROTA

Advertisement

Yan matan Zamfara sun sake samun ‘yanci bayan watanni bakwai da aka yi garkuwa da su

An ruwaito cewa babu wani sashin doka da ya bayyana inda jami’an KAROTA za su yi amfani da Gora, “don haka ba za mu sauka daga tsarin doka mu yi abunda ya saɓa da tsarin dokar ba.

Al’umma sun jima suna korafi kan yadda jami’an na KAROTA ke amfani da Gora yayin da suke gudanar da aiki.

Advertisement

Haka kuma, a baya an sha samun rikici da wasu daga cikin jami’an bisa yi wa masu ababen hawa ta’adi, yayin da suke amfani da Gorar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending