News
Indaranka:Matukin jirgin sama ya mutu a bandaki dauke da fasinjoji 271
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Wani matukin jirgin sama ya mutu bayan ya fado a bandakin wani jirgin sama na Miami zuwa Chile tare da fasinjoji 271.
Jaridar Independent ta rawaito cewa Kyaftin Ivan Andaur ya fara jin rashin lafiya sa’o’i uku a cikin jirgin LATAM Airlines daga Florida zuwa Santiago kuma bayan ya fadi a bandaki kuma ya samu kulawar gaggawa daga ma’aikatan jirgin.
Wani mutum dan shekara 35 ya rataye kansa saboda tsadar rayuwa a Jigawa
Jirgin ya dauki mintuna 30 kafin ya karkata zuwa filin jirgin saman Tocumen na birnin Panama.
Andaur, tsohon matukin jirgin sama ne wanda yayi shekaru 25 yana aiki, ya mutu lokacin da jirgin ya sauka.
Jirgin LA505, wanda ke aiki da Boeing 787-9 Dreamliner, ya bar Miami da karfe 10.11 na ranar Litinin 14 ga Agusta kuma yana da kyaftin din agaji da jami’in farko a cikin lokacin da lamarin ya faru.
“Rukunin kamfanonin jiragen sama na LATAM sun ba da rahoton cewa jirgin LA505 a jiya, wanda ke kan hanyar Miami-Santiago, ya sauka a filin jirgin sama na Tocumen a Panama saboda gaggawar likita ga daya daga cikin ma’aikatan jirgin uku.
Alokacin da jirgin ya sauka, jami’an agajin gaggawa sun ba da taimakon ceton rai, amma matukin jirgin ya mutu.
