News
Tinubu ya mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a Gabon.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani kan juyin mulkin da aka yi a Gabon,inda aka yi wa Shugaba Ali Bongo daurin talala.
Idan dai za a iya tunawa, wasu jami’an soji sun kulla makarkashiyar kwace mulki daga hannun Bongo bisa abin da suka kira kurakurai da aka gani a babban zaben kasar da aka yi a tsakiyar Afirka.
Wani mutum ya kashe mahaifinsa mai shekaru 100 har lahira akan N70,000
Jami’an sun kuma amince cewa gudanar da babban zaben kasar na ranar 26 ga watan Agusta, 2023, bai cika sharuddan gudanar da zabe na gaskiya kamar sahihanci da hada kai da al’ummar Gabon ke fata ba.Har ila yau, sun yi nuni da rashin gaskiya da rashin tabbas, wanda ya haifar da ci gaba da tabarbarewar zamantakewar al’umma, tare da kasadar kai kasar cikin rudani.
Amma da yake mayar da martani a madadin shugaba Tinubu a ranar Laraba, mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale, ya ce fadar shugaban kasar na sa ido sosai tare da nuna matukar damuwa “da alamun rigimar mulkin kama karya da ke yaduwa a yankuna daban-daban na nahiyar afirka.”
Ya ce shugaban kasar “ya tabbatar da cewa bin doka da oda a kan kudurorin tsarin mulki da kayan aikin warware takaddamar zabe ba dole ba ne a bar su a kowane lokaci su halaka daga babbar nahiyar afirika ba
“Don haka, shugaban kasar yana gaba da tattaunawa da sauran shugabannin kasashen Afirka don cimma matsaya daya kan matakai na gaba game da yadda ikon kasar Gabon zai kasance da kuma yadda nahiyar za tga mulkin kama-karya mai yaduwa da muka gani ya bazu a nahiyarmu.
