News
Jagoran mulkin sojan Kasar Gabon ya gana da jam’iyyun siyasar ƙasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Jagoran mulkin soja a kasar Gabon, Birgediya Janar Brice Oligui Nguema, ya gana da shugabannin jam’iyyun siyasar ƙasar a yunƙurin da yake yi na mayar da mulki ga farar hula.
Gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar ya nuna jagororin siyasar a ranar Asabar suna roƙon sojan da ya tabbatar sabuwar gwamnatin riƙon-ƙwaryar da za a kafa ta tsara “tsarin shari’a” da zai ba da damar komawa kan turbar dimokuraɗiyya.
Yan sanda sun kammala bincike kan mutuwar wani yaro dan shekara 17 a Adamawa
Janar Nguema ya nemi jam’iyyun su shiga a dama da su a shirin miƙa mulkin ta hanyar ba da gudummawarsu a zaɓe da kuma tsara kundin mulki “da zai ƙunshi ra’ayin al’ummar Gabon”.
“Daga yanzu ba za mu so mu dinga ganin ‘yan siyasa uku ko huɗu sun taru ba kuma su sauya wani tsari da gwamnati za ta bi, kuma daga baya mu ji an ce an amince da sauya tarin zaɓe a taron ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.
Gwamnatin Ali Bongo da aka hamɓarar ta aiwatar da sauye-sauye masu cike da cecekuce a tsarin zaɓen ƙasar wata ɗaya kafin zaɓen ƙasar ranar 26 ga watan Agusta, wanda aka ce wasu jam’iyyun adawa ne suka nemi a yi hakan.
