News
Yan sanda sun kammala bincike kan mutuwar wani yaro dan shekara 17 a Adamawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Afolabi Adeniyi, ya fara gudanar da bincike kan zargin kisan wani yaro dan shekara 17, Abdullahi Abba, wanda ake kira Abdallah, bisa umarnin gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce za a bayyana rahoton binciken ta a ranar Litinin mai zuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Suleiman Ngurore ya bayyana cewa an kammala bincike kan lamarin kisan kai.
“Zan iya tabbatar muku cewa an kammala bincike kuma za a fitar da rahoton ranar Litinin.”
Advertisements
