News
Kungiyar Lauyoyin Ta Yaba Da Matakin Gwamnatin Kano Kan Korar Wasu Mukarrabansa.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakin gaggawa da ya dauka na korar wasu mukarrabansa guda biyu sakamakon barazanar kisan alkalan kotunan sauraren kararrakin zaben da kuma kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa.
Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa kwamishinan kasa da safayo, Adamu Aliyu Kibiya a wani taron addu’a na musamman da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka gudanar inda ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da cewa duk wanda a cikinsu ya karbi cin hanci don murde hukuncin sai dai ya zabi ko kuɗi ko rayuwarsa.
Rundunar Yan Sandan Jahar Gombe Tace Mutum 67 Ne Suka Bace Cikin Watanni Tara
Har ila yau mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni, Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Boye a wani faifan bidiyo a ranar Alhamis yayin taron addu’o’i na musamman da NNPP ta gudanar yayi kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa, Khasim Shettima da kuma tunzura al’umma.
Da yake zantawa da manema Labarai Shugaban kungiyar lauyoyin na Kano Barista Sagir Gezawa ya yaba wa gwamnan kan matakin korar mukararaban nasa kan kalaman da sukai da kuma nisanta gwamnatinsa da kalaman da sukai .
Daga nan Gezawa ya yi kira ga jami’an tsaro da su kaddamar da bincike kan barazanar kisa da kwamishinan ya yi wata kila akwai wata makarkashiya a cikin wannan barazanar ta shi.
Wani labarin kuma Abba Ya Gargadi Makarantu Kan Kara Kudin Makaranta
A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.
A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.
Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.
Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
