Connect with us

News

Abba Ya Gargadi Makarantu Kan Kara Kudin Makaranta

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya gargadi makarantu a jihar Kano da kada su kuskure su kara kudin makaranta da na littattafai yayin da ake komawa sabon zangon karatu.

Advertisement

Gwamnan ya bayyana hakan ta bakin mai ba gwamnan jihar Kano shawara ta musamman kan makarantun masu zaman kansu, Baba Umar.

Rundunar Yan Sandan Jahar Gombe Tace Mutum 67 Ne Suka Bace Cikin Watanni Tara

Baba Umar ya gargadi mamallakan makarantu masu zaman kansa wadanda ke cajin kudin makaranta da yawa ba bisa ka’ida ba da su daina.

Ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ba za ta nade hannayenta ta bari a ciki gaba da irin wannan abu ba.

Advertisement

Baba Umar wanda ya yi gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Juma’a, 15 ga watan Satumba, ya ce daga yanzu babu wani mai makaranta da aka ba damar kara kudin makaranta ba tare da ya bi ka’idojin da aka shimfida ba.

Haka kuma ya ce daga yanzu babu masu makarantar da ke da damar tilasta iyaye siyana litattafai da inifam daga makarantunsu.

A cewarsa, duk masu yin kakkausar suka ga gwamnati kan matakan da ake dauka don duba abubuwan da shugabannin makarantu ke yi , suna yin hakan ne domin kare ayyukansu da suka sabawa doka.

Advertisement

Hadimin gwamnan ya ci gaba da cewa, duk shugaban makarantar da bai gamsu da matakan da gwamnati ta dauka don tsaftace tsarin ba, toh ya nemi a yi shari’a.

Wani labarin kuma Rundunar Yan Sandan Jahar Gombe Tace Mutum 67 Ne Suka Bace Cikin Watanni Tara

 

Advertisement

A yayin da ake cigaba da samun cikas wajen balaguro a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas, biyo bayan komawar da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje suka yi zuwa sabuwar tashar jiragen sama, gwamnatin tarayya ta gayyaci kamfanonin jiragen sama na kasashen waje zuwa wani taro a yau.

 

A sakamakon haka, kwamitin da ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya kafa domin duba rudanin tafiye-tafiye a filin jirgin sama naMurtala Muhammad da kwamitin ministoci zai gana da masu ruwa da tsaki a domin nemo bakin zaren da warware matsalar.

Advertisement

 

Fasinjojin kasa da kasa da suka tashi daga Najeriya a ranakun Laraba da Alhamis sun makale a biranen Legas da Cairo da Doha da Landan, da sauran wurare bayan da madaurin kaya na jirgi ya lalace a sabon filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas, al’amarin da ya tilastawa kamfanonin jiragen sama jinkirtawa tare da soke tashin jirage.

 

Advertisement

Har yanzu zuwa karshen mako matsalar tafiye-tafiye na ci gaba da wanzuwa inda fasinjojin ke kwashe sa’o’i a kan layi domin tantance su ta hanyar binciken tsaro

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *