Connect with us

News

Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Majalisar dokokin Jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi na  ‘YanKwashi ya Birniwa da kuma Gumel bisa zargin su da rashin da’a.

Shugaban kwamitin kananan hukumomi a majalisar Honarabul Aminu Zakari shine ya tabbatarwa wakilin mu na Dutse hakan.

Advertisement

NLC, TUC Sun Yabawa Gwamna Sani kan sakin naira biliyan 3.1 Ga ‘Yan Fansho a Kaduna

Yace dakatarwar ta biyo bayan tafiya kasar Rwanda da shugabannin kananan hukumomin uku sukayi, da kin halartar gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 da gwamna yayi a gaban majalisar.

Alh Aminu Zakari ya bayyana cewa an kafa kwamiti karkashi jagorancin shugaban masu rinjaye na majalisar honarabul Lawan Muhammad Dansure domin yayi bincike kan dalilin da ya hana ciyamomin zuwa gabatar da kasafin kudin duk da mahimmacin sa ga jiha.

Advertisement

Ya kuma kara da cewa shugabannin kananan hukumomi 9 sun tafiya amma shida daga cikin su sun dawo domin halartar gabatar da kasafin kudin, yayinda ragowar ukun suka ki dawowa.

 

Advertisement

 

sawaba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending