Politics
Za mu yi ta gwagwarmaya har sai an tabbatar mana da kujerar gwamnanmu – NNPP
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa ta NNPP ta nemi majalisar kula da alkalai ta kasa NJC ta yi bincike game da batun zaman gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf cikakken dan jam’iyyar mai rijista.
Shugabancin jam’iyyar ya ce Abba Kabir ya yi rijista a ranar 27 ga watan Maris 2022 a mazabar Diso-Ciranci da ke karamar hukumar Gwale.
Yan Sandan Sun Kama mutum shida ’yan gida daya Da Suka Yiwa Alkali dukan kawo wuka A Gombe.
NNPP ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ta kira a yau Laraba cikin Abuja, babban birnin kasar.
Taron na zuwa ne kwanaki kalilan bayan hukuncin kotun daukaka kara da ya soke nasarar Gwamna Abba Kabir a zaben watan Maris, bisa hujjar cewa bai cika ka’idar tsayawa takara ba, saboda babu sunansa a rijistar NNPP a lokacin.
Bbc ta ruwaito cewa NNPP ta ce za ta ci gaba da gwagwarmaya don ganin an tabbatar mata da kujerar gwamnan Kano.
A cewarta, Abba Kabir Yusuf ya bi duk wani mataki na kasancewa dan jamiyya, kama daga tantancewar da aka yi a watan Mayun 2022, zuwa zaben fidda gwani a watan Yuni, wanda ya kai ga zabarsa a matsayin dan takarar NNPP.
A wani labarin kuma Yan Sandan Sun Kama mutum shida ’yan gida daya Da Suka Yiwa Alkali dukan kawo wuka A Gombe.
Kamar yadda muke kawo rahoto, an fahimci cewa matakin dakatar da fadan zai fara aiki daga gobe Alhamis da karfe 10 na safe, agogon Gaza.
‘Yan sa’o’i kalilan da suka wuce, ana ci gaba da kara mayar da martani kan harkokin diflomasiyya. Ga wasu muhimman muryoyi da muka ji.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi maraba da yarjejeniyar dakatarwar, amma ya kara da cewa: “Wannan bai isa kawo karshen wahalar da fararen hula ke ciki ba” yayin da yake kira a kara kokari don ci gaba da sakin sauran mutanen da ake garkuwa da su sannan a tsagaita wuta a Gaza.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce wannan al’amari wani “muhimmin mataki ne da ya dace, sai dai akwai bukatar kara kokari.”
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce kasar na fatan yarjejeniyar za ta iya taimakawa wajen kawo cikakken karshen yakin, kuma ta “fara wani yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa a kan ginshikin masalahar kafa kasa biyu.”
Can kuma, Sarki Abdullahi na Jordan yana jagorantar wata tattaunawa da Shugaban Masar Abdel Fattah al Sisi a kan yadda za a kawo karshen “aukawar Isra’ila kan Falasdinawa da yaki”, wata sanarwar fadar Sakin ta ce.
