Politics
Muna maraba da kafa jam’iyyar haɗaka kamar yadda Atiku ya nema – NNPP
Jam’iyyar adawa ta nuna aniyarta ta shiga jam’iyyar haɗaka da sauran jam’iyyun adawa kamar yadda Atiku Abubakar ya nema a makon da ya gabata.
Ɗan takarar na jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban Najeriya na 2023, Atiku ya zargi APC da yunƙurin mayar da Najeriya bin tsarin jam’iyya ɗaya sannan ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su dunƙule don yin waje da jam’iyyar mai mulki.
Gwamnan Kano ya sake gabatar da wani ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin na biliyan 24
Shugaban riƙo na NNPP na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya faɗa a yau Talata yayin wani taron manema labarai cewa kiran na Atiku abin a yaba ne.
“NNPP na kallon wannan kira na Atiku a matsayin na kishin ƙasa kuma abin maraba,” in ji shi. Sai dai ya ce suna so a yi wa shirin kwaskwarima.
“Sai dai kuma NNPP na son a sauya wa shirin fuska. Muna ganin ya kamata abin ya ƙunshi kowa da kowa, kuma a faɗaɗa shi. Irin wannan haɗakar jam’iyyu suka yi a 2015 wadda ta ba su damar kayar da jam’iyya mai mulki ta PDP a lokacin.
“Saboda haka muna ganin kiran da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubkar ya yi abin yabawa ne.”
A wani labarin kuma Gwamnan Kano ya sake gabatar da wani ƙwarya-ƙwaryan kasafin kudin na biliyan 24
Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu ta yanke hukuncin rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Pretoria tare da dakatar da duk wata hulɗar diplomasiyya tsakaninta da ƙasar.
Majalisar ta ɗauki matakin ne har sai Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza tare da hawa teburin sasantawa.
Jami’iyar ANC mai mulki, wadda take da rinjaye a majalisar dokokin ƙasar, ta kwatanta gwagwamayar Falasɗinawa da irin wadda Afirka ta Kudu ta sha lokacin da suke fafutikar neman ƴancin kai daga fararen fata.
Wakilin BBC ya ce gabanin kaɗa ƙuri’ar, Isra’ila ta yi wa jakadanta kiranye, inda ta ce za ta tattauna da shi .
