News
Bangaren Shari’a Zai Iya Rasa Kimarsa A Idon ‘Yan Nijeriya -Bode George
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani jigon jam’iyyar PDP, Cif Olabode George, ya yi Allah-wadai da matakin da alkalai suka dauka na soke nasarar zaben ‘yan siyasa.
George yana maida martani ne kan cece-kucen da kotun daukaka kara ta yanke a jihar Kano.
Ronaldo ya bukaci Alkalin wasa ya soke Fenality da ya bashi bayan ya gano akwai kuskure
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa kotun daukaka kara ta soke zaben gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, yayin da ta bayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar.
Amma rudani ya barke lokacin da Certified True Copy, CTC, na hukuncin ya nuna cewa kotun daukaka kara ta tabbatar da Yusuf a matsayin gwamnan Kano.
Amma Kotun Daukaka Kara ta danganta hakan da tuntuben alkalami da kuma rashin fahimta.
Da yake mayar da martani, George ya ce abin damuwa ne yadda ‘yan Najeriya suka daina amincewa da bangaren shari’a.
Da yake jawabi ga taron manema labarai a Legas a ranar Litinin, jigon na PDP ya ce,wannan tsarin yana da matukar damuwa domin idan mutane ba su yarda da bangare na uku na gwamnati ba, rikici ya kunno kai.
Tabbas, kawancen da ake yi tsakanin wasu ‘yan siyasa da alkalai yana da hadari ga dimokuradiyyar mu.
