News
Rundunar Soji Ta Kama Wasu Sojoji 3 Da Laifin Sata A Jihar Borno

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dakarun ‘Operation Desert Sanity’ da ke garin Maiduguri sun damƙe wasu sojoji uku bisa zargin su da satar alburusai.
Sojojin dai an kama su ne a wani samame da aka kai a tashar mota dake kan titin Njimtilo a Maiduguri.
An bayyana cewa ɗaya daga cikin sojojin a cikin kwanon awon shinkafa ya ɓoye alburusan da ya sata.
Wikki Time ta ruwaito cewa Ga abinda majiyan tace, “A ranar 2 ga watan Disamba, 2023, sojoji sun gudanar da simamen sirri a tashoshin motoci da kuma kan hanyar Njimtilo, inda aka kama sojoji uuku.Ɗaya daga cikin su an kama shi ne a kan hanyar sa ta zuwa garin Makurɗi da alburusai 250 RDS masu 7.62 mm.
Haka kuma shima Ɗayan sojin an kama shi ne a hanyar sa ta zuwa Makurɗi tare da alburusai masu zagaye 110 wanda ya ɓoye a cikin kwanon awon shinkafa.
Shi kuma na ukun an kama shi ne a hanyar sa ta zuwa Abuja. Inda aka same Shi da zagaye 14 na alburusai masu 7.62mm.
Waɗanda ake zargin yanzu haka suna tsare domin ci gaba da bincike. ”
Ba a sami damar jin ta bakin Darakta, ayyukan da yaɗa labarai a harkar tsaro, Maj-Gen. Buba Edward,
Kawo izuwa lokacin haɗa wannan rahoto Daraktan bai sami damar ɗaga kiran waya da aka yi masa ba,Jaridar Leadership ta bayyana.
