Connect with us

News

Yan Bindiga Ya Kamata A Jefawa Bam,Ba Masu Taron Mauludi Ba -Shehu Sani

Published

on

Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani
Advertisements
ads

DAGA UMMAR IBRAHIM HOTORO 

 

Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya yi Allah-wadai da harin da sojoji suka kai ta sama wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Martanin Sani ya biyo bayan tabbacin da rundunar sojin Najeriya ta yi na cewa ita ce ke da alhakin harin da aka kai ranar Lahadi.

Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Tabbatar Da Cewa Su ne Suka Yi Luguden Bama bamai ga Mazauna Wani Kauye a Kaduna

Ya ce kamata ya yi a jefa wadannan bama-bamai kan ‘yan ta’adda ba farar hula ba.

DAILY POST ta ruwaito cewar wani jirgi mai saukar ungulu mara matuki ya kai harin bama-bamai a wasu sassan al’umma, inda har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba a daidai lokacin da mutanen kauyen ke gudanar da bukukuwan Mauludi na tunawa da haihuwar Annabi Muhammad.

Advertisement

Wani rahoto daga kauyen Kaduna da aka jefa bama-bamai kan mabiya addinin ya nuna cewa sama da mutane 150 ne suka mutu.

Mummunan aiki ne sojojin Nijeriya suka yi,domin ya kamata a jefa wadannan bama-bamai kan ‘yan ta’adda ba farar hula ba,” Sani ya rubuta a shafinsa na X ranar Litinin.

A wani labarin kuma Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Tabbatar Da Cewa Su ne Suka Yi Luguden Bama bamai ga Mazauna Wani Kauye a Kaduna

Ma’aikatar lafiya a Gaza da ke ƙarkashin kungiyar Hamas ta sanar da cewa mutane 15,899 ne suka mutu a yankin tun bayan da Isra’ila ta fara yakin ramuwar gayya kan hare-haren na ranar 7 ga Oktoba.

Sun ce mutum 349 ne aka kashe a hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar Lahadi.

Hamas ta ce kashi 70 cikin 100 na mace-macen mata ne da yara kanana.

Advertisement

Isra’ila ta ce manufarta na rikicin shine kawar da kungiyar Hamas daga Zirin Gaza bayan da ƴan bindigan Falasɗinawa suka tsallaka kan iyakar ƙasar zuwa Isra’ila tare da kashe mutane 1,200 da kuma kama mutum 240.

An sako sama da mutane ɗari da aka yi garkuwa da su a lokacin da aka tsagaita buɓe wuta na wucin gadi na kwanaki bakwai.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending