News
Babu Wani Umarni Da Kotu Ta Bayar Na Binciken Lafiyar Gwamna Akeredolu – Gwamnatin Jihar Ondo
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Ondo ta yi watsi da rahotannin baya-bayan nan da ke nuni da cewa akwai wani umarnin kotu da ya umarci majalisar dokokin da kakakinta Olamide Oladiji da su kafa kwamitin lafiya domin tantance lafiyar Gwamna Rotimi Akeredolu.
Gwamnatin ta bayyana rahoton amatsayin na bogi, inda ta ce abunda ake yadawa bai yi daidai da shari’ar da kotuna ke ci gaba da yi akan al’amarin ba.
Kotu Ta Daure Wani Jigon Jam’iyyar APC A Jihar Legas Saboda Laifin Sayen Kuri’u A Zaben 2023
A wata sanarwa da babban mai shari’a na Ondo, Charles Titiloye ya fitar, ya ce kotun ta bayar da wani izini ne kawai ga lauyoyi da kuma bangarorin shari’ar.
Titiloye ya ce ba a baiwa gwamnatin jihar Ondo bayanai kan zaman kotu ba ko kuma ta samu damar gabatar da nata bangaren ba kan al’amarin.
Wani labarin kuma Kotu Ta Daure Wani Jigon Jam’iyyar APC A Jihar Legas Saboda Laifin Sayen Kuri’u A Zaben 2023
Amurka ta soki yadda Isra’ila ke yaƙi a zirin Gaza, a daidai lokacin da aka shiga watanni biyu da ɓarkewar yaƙin tsakaninta da Hamas.
Sakataren harkokin wajen Amurka ya ce Isra’ila ba ta cika alƙawarin da ta ɗauka na kare farar hula a yaƙin da ta ke ƙara zafafawa a Gaza ba, idan aka kwatanta da halinda ake ciki a yanzu.
Anthony Blinken ya shaidawa manema labarai a Washington cewa, akwai matakai da dama da Isra’ila ya kamata ta ɗauka domin tabbatar da cewa Falasdinawa Farar hula sun isa tudun mun tsira cikin nutsuwa.
Mr Blinken ya ce ba wai kawai su isa wurare masu aminci kaɗai ba, har da yi musu bayanin inda ya kamata su nufa, da lokacin da za su tafi, suna buƙatar abubuwa kamar ruwan sha da abinci da magani.
Babban jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce yana fatan buɗe iyakar Isra’ila da Kerem Shalom ka iya sauƙaƙa kai kayan agaji cikin sauri ga Falasdinawa.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
