News
Zanga-Zanga Ta Barke Yayinda ‘Yan Bindiga Suka Sake Sace ‘Dalibai A Jami’ar Tarayya Ta Nasarawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wasu ‘yan bindiga sun sake kai farmaki unguwar Gandu tare da yin garkuwa da wasu dalibai a jami’ar tarayya da ke Lafia.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, da farko ‘yan bindigar kai harin cikin ayari da karfe 7:30 na Almuru a ranar Laraba, amma sai suka gudu suka shiga daji domin buya na tsawon sa’o’i da dama bayan da suka lura da jami’an tsaro.
Babu Wani Umarni Da Kotu Ta Bayar Na Binciken Lafiyar Gwamna Akeredolu – Gwamnatin Jihar Ondo
Sun sake tasowa da tsakar daren ranar alhamis daura da ginin jami’ar, inda suka kwashe kimanin sa’o’i uku suna gudanar da ayyukansu cikin walwala, daga bisani suka yi awon gaba da dalibai biyar a yayin da da dama suka samu raunuka.
Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, kakakin jami’ar, Abubakar Ibrahim, ya ce har yanzu ba a tantance adadin daliban da aka sace ba amma ya ce dalibai uku ne zuwa biyar.
Arewa Radio ta rawaito cewa A wani bangaren kuwa, daliban jami’ar ta Lafiya dake Jihar Nasarawa sun gudanar da zanga-zangar lumana a ranar Alhamis, inda suka bukaci a kawo karshen yawaitar harin garkuwa da dalibai da ake yi a yankin.
Rahotanni sunce an sace dalibai sama da 15 na jami’ar a wannan zangon karatu tare da biyan makudan kudin fansa a cikin mawuyacin hali.
Daya daga cikin wadanda harin da aka kai a baya ya rutsa da su, ya shaida wa jaridar daily trust cewa ‘yan bindigar sun lakadawa biyar daga cikin su da aka yi garkuwa da su duka tare da yi musu barazana a cikin dare har wayewar gari.
Wanda abin ya shafa ya kara da cewa daga baya sun karbi Naira dubu 500 daga hannun iyayensa suka sake shi, yayin da bai san abin da ya faru da sauran ba saboda ba za su iya biya ba.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
