Connect with us

News

An kashe ‘yan Najeriya sama da dubu 5 tun bayan darewar Tinubu kan mulki

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

An kashe ‘yan Najeriya sama da dubu 5, yayin da aka sace dubu 2 da 263 tun daga lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dare kan karagar mulki a cikin watan Mayun da ya gabata.

FRI  Hausa ta ruwaito cewa Kamfanin Beacon Consulting da ke nazari kan matsalar tsaro ya bayyana haka a cikin wani rahoto da ya fitar a daidai lokacin da ‘yan bindiga suka zafafa hare-harensu kan al’umma musamman a jihohin arewacin Najeriya.

Advertisement

Rahoton ya ce, a cikin watan Yuni kadai na wannan shekarar, an kashe ‘yan Najeriya har guda 854, inda a cikin watan Yuli aka kashe 552, yayin da a cikin watan Agusta aka kashe 638.

Sai kuma wadanda aka kashe a cikin watan Satumba da adadinsu ya kai 581, sai kuma a cikin watan Oktoba da aka kashe dubu 1 da 127, yayin da aka kashe dubu 1 da 308 a cikin watan Nuwamban da ya gabata.

Advertisement

Kamfanin na Beacon Consulting ya zargi gwamnatocin Najeriya da gazawa wajen aiwatar da sauye-sauyen da ake bukata domin ingnata sha’anin tsaro a kasar

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu ya kori shugaban FAAN, NiMet da wasu Ma’aikatu

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending