News
Da hannun wasu ‘manyan ƙasa’ cikin ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda a Nijeriya -Minista
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan Ma’adinai, Mr Dele Alake, ya bayyana cewa da hannun wasu manyan ƙasa a harkar ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda da haƙar ma’adinai ta ɓarauniyar hanya a Nijeriya.
Jaridar Blueprint ta rawaito cewar, Alake ya yi wannan tonon sililin ne sa’ilin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Ma’adinai don kare kasafin ma’aikatarsa na shekarar 2024 a Abuja.
An kashe ‘yan Najeriya sama da dubu 5 tun bayan darewar Tinubu kan mulki
Kazalika, Ministan ya yi zargin akwai baƙi da ke haƙar ma’adinai a Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.
Don haka ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta maida hankali sosai kan fannin ma’adinai wanda ka iya samar wa ƙasa biliyoyin Naira duk shekara.
Sama da shekara 13 ‘yan ta’adda na addabar shiyoyin Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas, tsakiyar Nijeriya da sauran sassan ƙasar.
‘Yan ta’addan sun yi ƙarfin da a wasu lokutan sukan kai hari su mamaye ƙauyuka inda suka nemi kuɗin fansa bayan sun yi garkuwa da mutane. Wasu lokutan kuma sukan ƙona gidajen jama’a bayan sun kwashi dukiya.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
