News
Wani Mutum Ya Halaka Kansa Ta Hanyar Rataya A Jihar Adamawa
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
A karo na biyu ckin kasa da mako guda an sake samun wani babban mutum mai shekaru mai suna, Yakubu Mamza, da ya kashe kansa a Jihar Adamawa.
Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da wata mata mai suna, Florence Vandi, ta kashe kanta a Unguwar Viniklang da je cikin Karamar Hukumar Girei ta Jihar Adamawa a sakamakon mutuwar saurayinta, lamarin da ya dagawa jama’a hankali, yanzu kuma ga mutum a karo na biyu shi ma ya rataye kansa.
Gawuna zai mayar wa yan kasuwar Kano wuraren su da aka rushe musu, in an gama Shari’a – Aruwa
Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Yi Ajalin Mutane 2 A Adamawa
Al’ajabi: Saurayi Ya Yi Wa Zakara Fyade A Adamawa
Yakubu Mamza, wanda ke zaune a wani ginin da ba a kammala aikinsa ba a Unguwar rukunin gidaje 80 da ke Jimeta, ya kashe kansa a cikin gidan da yake kwana, ya rasu ya bar yaya da mata uku.
Leadership ta ruwaito cewa marigayi Yakubun, shekaru biyu kenan basa tare da matarsa, yana zaune shi kadai a cikin wannan ginin da ba a kammala aikinsa ba.
Kawo lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance dalilin da yasa ya rataye kansa ba, haka kuma rundunar ‘yansandan jihar ba ta ce uffan ba game da mutuwar Yakubu ba.
A wani labarin kuma Gawuna zai mayar wa yan kasuwar Kano wuraren su da aka rushe musu, in an gama Shari’a – Aruwa
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
