News
Shugaba Tinubu Ba Zai Iya Dawo Da ‘Yan Majalissar Dokokin Jihar Rivers 27 Kan Kujerunsu Ba – Femi Falana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yayin da ake ci gaba da mayar da martani kan tsoma bakin shugaba Bola Tinubu kan rikicin da ya dabaibaye jihar Rivers, lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya ce shugaban kasar ba zai iya mayar da ‘yan majalisar dokokin jihar su 27 da ke fuskantar takaddamar Sauya she’ka ba.
A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Falana, babban lauyan Najeriya mai kwarewar SAN, ya ce tilas ne a ko da yaushe tsoma bakin shugaban kasa ya kasance bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.
Kungiyar Kwadago ta NLC za ta yi gagarumar zanga-zanga kan karancin takardun kudi a Nijeriya
A cewarsa, tuni aka ayyana kujerun ‘yan majalissar a matsayin wadanda babu kowa kamar yadda doka ta yi tanadi.
Har ila yau, ya zama wajibi INEC ta gudanar da zaben da zarar an soke umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Ya ce ‘yan majalisar da ke rike da madafun iko za su iya rike kujerunsu ne kawai idan sun tabbatar da cewa jam’iyyar siyasar da suka ci zabe a karkashinta d ta rabu gida biyu ko fiye da haka.
A wani labarin kuma Kungiyar Kwadago ta NLC za ta yi gagarumar zanga-zanga kan karancin takardun kudi a Nijeriya
Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.
Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar
Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.
Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara
Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.
Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.
Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.
