Connect with us

News

Gwamna Abba Ya Gabatarwa Majalissa Sabbin Nade-Nade A Hukumar Zabe KANSIEC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya mika jerin sunayen mutane takwas da zai nada a matsayin mambobin gudanarwa na hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Advertisement

Kakakin majalisar, Alhaji Ismail Falgore, ya karanta wasikar Yusuf a zaman majalisar a ranar Talata a Kano, ya kuma umarci wadanda aka nada su bayyana a gaban ‘yan majalisar domin tantance su a ranar Alhamis.

Shugaba Tinubu Ba Zai Iya Dawo Da ‘Yan Majalissar Dokokin Jihar Rivers 27 Kan Kujerunsu Ba – Femi Falana

Hakazalika, gwamnan ya kuma gabatar da jerin sunayen karin masu bada shawara na musamman guda 10 ga majalisar domin tabbatar da su.

Advertisement

Falgore ya mika jerin sunayen ga kwamitin majalisar kan al’amuran zabe.

A wani bangaren, kwamitin majalisar kan kasafin kudi ya mika rahotonsa kan kasafin kudin shekarar 2024 ga majalisar.

Advertisement

A wani labarin kuma Shugaba Tinubu Ba Zai Iya Dawo Da ‘Yan Majalissar Dokokin Jihar Rivers 27 Kan Kujerunsu Ba – Femi Falana

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Advertisement

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman alumma da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar.

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Advertisement

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Masu iya magana na cewa Shari’a mace ce da ciki ba’asan wa Zata Haifa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending