News
Da Dumi Dumi: Hukumar Zaben Kano Ta Rage Kudin Fam Din Takarar Zaben Kananan Hukumomi Biyo Bayan Umarnin Kotu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano, KANSIEC, ta rage kudin fam din takarar zaben kananan hukumomi, biyo bayan umarnin kotu.
Hukumar ta sanar da ragiwar ne a hedikwatarta da ke Kano, inda ta bayyana cewa a yanzu masu neman kujerar shugabancin chairman za su biya Naira miliyan 9, yayin da wadanda ke neman kujerar kansila za a karba Naira miliyan hudu.
Rage kudaden ya biyo bayan hukuncin da wata kotu ta yanke wa wasu jam’iyyun siyasa uku da suka kalubalanci matakin da KANSIEC ta dauka na karbar naira miliyan 10 na fom din takarar .
Duk da cewa wasu jihohin Najeriya na karbar kudi har Naira miliyan 20, hukumar ta Kano ta bi umarnin kot.
Farfesa Malumfashi ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa harkokin zabe a matsayinsu na masu ruwa da tsaki.
