Connect with us

News

Akalla Mutane 21 Ne Suka Mutum Sanadiyyar  Hatsarin Mota Da Ya Afku A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja 

Published

on

Akalla Mutane 21 Ne Suka Rasa Rayukansu A Wani Hatsarin Mota Da Ya Afku A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kaduna zuwa Abuja tsakanin kan iyakar jihohin Kaduna da Neja a ranar Alhamis.

Channels tv ta ruwaito cewa hatsarin ya hada da wata babbar mota da wata motar bas da ta nufi Kano daga Abuja da jihar Katsina.

Da Dumi Dumi: Hukumar Zaben Kano Ta Rage Kudin Fam Din Takarar Zaben Kananan Hukumomi Biyo Bayan Umarnin Kotu

Wata majiya daga hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Kaduna, ta bayyana cewa hatsarin ya afku ne sabida lalacewar Hanyar.

lamarin da ya tilastawa duk motocin da suke tahowa daga sassan daban-daban yin tuki ta hanya daya sakamakon kyaran titin. Titin Kaduna zuwa Abuja wanda ya dauki lokaci mai tsawo ba a kammala shi ba .

A cewar jami’in FRSC, nan take direban motar ya gudu daga inda hatsarin ya afku, wanda hakan ya haifar da cunkoson ababen hawa da suka taru a kan babbar hanyar da ta dauki tsawon sa’o’i da dama.

Advertisement

An garzaya da fasinjoji uku da suka tsira zuwa asibitin tunawa da Umaru Musa da ke garin Sabon-Wuse, kusa da kan iyaka tsakanin jihohin Kaduna da Neja domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending