News
Sojoji Sunyi Nasarar Kashe ƙasurgumin Dan Bindigar Nan Daya Addabi Arewacin Nageriya
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Rundunar Sojojin Nijeriya sun tabbatar da Kashe Halilu Buzu wanda akafi sani da Halilu Sububu ƙasurgumin ɗanbindigar da jami’an tsaron Najeriyar ke nema ruwa a jallo dake yankin Jihar Zamfara.
An Kashe ɗanbindigar ne bayan ɗauki ba ɗaɗi tsakaninsu da wani gungun ƴan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanci a ƙananan hukumomin Zurmi da Anka.
Ɗanjarida a yankin wanda ya tattaro bayanai kan abin da ya faru, Mannir Fura Girke ya shaida wa kafar yada labarai ta BBC yadda al’amarin ya faru.
“Ya ce Jami’an tsaro sun samu bayanan sirri da ke nuna cewa ƙasurgumin ɗan bindiga Kachalla Halilu Sububu zai wuce da tawagarsa. Yana tafiya da rakiyar ƴanbindiga fiye da 60 kuma inda tun Magribar yammacin Alhmais har zuwa asubar yau Juma’a.
A nan ne kuma akayi wannan ba-ta kashi kuma sojoji suka samu damar kashe shi tare da manyan kwamandojinsa bayan samun nasarar karɓe babura fiye da 20 da alburusai da sauran nau’in makamai.” In ji Fura Girke.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da hakan a shafinta na X, inda babban hafsan sojojin Najeriyar, Janaral Christopher Musa yake shaida wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Dare cewa “kwanan Bello Turji da sauran ƴan ta’adda ya ƙare kuma ya kamata kisan Halilu Sububu ya zama izna gare su.”
Wani bincike da jaridar PRNigeria ta yi ya nuna cewa Halilu Sububu ne ya kitsa kisan matuƙin jirgin nan mara matuƙi na hukumar farin kaya ta DSS kimanin watanni biyu da suka gabata.
