News
Masu shayi koko da kosai na zabga ciniki a garin Kano a dalilin yanayi na hunturu da aka shiga.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Masu shayi koko da kosai na zabga ciniki a garin Kano a dalilin yanayi na hunturu da aka shiga.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labarani Kasa da ya zagaya cikin garin Kano ya shaida cewa duka waɗanda ya zanta da sun bayyana masa cewa suna zabga ɗan karan ciniki a wannan lokaci.
Wani mai shayi Buba Musa a Dakata, ya bayyana cewa tun daga ƙarfe 6 na safe ake yin tururuwa teburi na asha shayi saboda sanyi.
” Ƴan a daidaita sahu da babura, acaba ne mafi yawan kwastamomi na. Tun da sanyin safiya suke tururuwa zuwa teburi na.
Musa ya kara da cewa akan siyar da kofin shayi ɗaya naira N100 ne ko kuma N200.
” Idan kuma kana so da indomie da kwai ne shima duk muma yi.
Wani mai yin shayi, Ali Sabo a titin Zoo, ya ce ya na ragargazar ciniki a sana’ar sa matuka yanzu saboda yanayi na hunturu da ake ciki.
Ya kara da cewa wata rana kwastamomi yawa suke musu.
Premium Times ta ruwaito cewa Hadiza Kabir mai yin koko da ƙosau a Kano ta ce harka fa ya buɗe masu a wannan lokaci.
” Ai mu cinikin Koko da Kosai ya buɗe man matuka a Kano. Mutane na garzayo wa tunda asuban farko su sha koko mai zafi da kosai.
“Ina yin ciniki fiye da yadda na ke yi a baya, wato kafin lokacin sanyi. Yanzu mutane na buƙatar abu mai zafi ne saboda yanayi na hunturu da ake ciki.
