Connect with us

News

Ina sane da sadaukarwar da yan najeriya suke yi saboda sauye-sauyen gwamnati -Tinubu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana sane da irin “sadaukarwar” da ‘yan ƙasar ke yi game da sauye-sauyen da gwamnatinsa take aiwatarwa tun bayan hawansa mulki a watan Mayu.

Cikin saƙon Kirsimeti da ya aika wa mabiya addinin Kirista, shugaban ya nemi ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin bikin da kuma hutu wajen “lura da ‘yan uwa saboda akwai waɗanda za su iya shiga cikin ƙunci, ko makoki, ko kuma waɗanda suka gaza cimma wani burinsu”.

Masu jiran a zartas masu da hukuncin kisa sun kai mutum 3,413 -Jami’in Kurkuku

Haka nan, ya bayyana 2023 a matsayin “shekarar sauyi a ƙasarmu”, yana mai cewa “ina sane cewa sauye-sauyen da suka zama tilas da muke aiwatarwa don samun ƙasa mai yalwa da arziki sun jawo sadaukarwa ta musamman”.

 

Ya ce: “Ina ƙarfafa muku gwiwa cewa nan gaɓa kaɗan, cikin jajircewarmu, za mu wayi gari cikin wata rana mai cike da zaman lafiya, da cigaba mai ɗorewa.”

Advertisement

 

Ya kuma nemi ‘yan Najeriya su yi amfani da damar wajen yi wa dakarun ƙasar maza da mata addu’a . “Allah ya kare su, ya mayar da su wajen iyalansu lafiya,” in ji shi.

 

Wannan ne bikin Kirsimeti na farko da shugaban zai yi a kan karagar mulki, wadda ta zo wa ‘yan Najeriya cikin ƙalubalen cire tallafin man fetur, da tsadar kayayyaki, da taɓarɓarewar matsalar tsaro.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending