Connect with us

News

Kada ku yi tsammanin samun sauƙi na gaggawa a halin yanzu – Adeboye

Published

on

Babban mai kula da cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG Fasto Enoch Adejare Adeboye

DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA

 

Babban mai kula da cocin Redeemed Christian Church of God, RCCG Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yi tsammanin samun sauki daga halin kuncin da kasar ke ciki nan ba da dadewa ba.

Fasto Adeboye ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da hasashen sa na sabuwar shekara a taron majami’ar da aka gudanar a sabon dakin taro na cocin da ke Simawa, jihar Ogun.

Babbar Magana: Zargin Fasto Bisa Ɗirkawa Wata Matashiya Ciki

Kalmominsa: “Kowane abin da Allah yake faɗi yana kan wannan ƙaramin jimla ne; Iska tana kadawa; ku hada a cikin addu’o’in ku cewa iska za ta yi muku kyau.

“A game da Nijeriya, ’ya’yana ƙaunatattu, abubuwa za su yi ta’azzara kafin su daidaita. Abubuwa za su yi zafi kaɗan kafin su huce. Domin iskar tana kadawa, wasu manyan sirrikan zasu bude.

Advertisement

Dattijai suna cewa “Idan iska ta buso, duburar kaza za ta fito.”

Malamin, ya shawarci ‘yan Najeriya da kada su karaya, ‘domin iska na kadawa, wanda kuma hakan na nufin abubuwa za su daidaita.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Game da hasashen sa guda ɗaya, Fasto Adeboye ya gaya wa ’yan cocinsa cewa su shirya don ƙwace damammaki da za su samu a wannan shekara: “Wasu mutane za su fara a matsayin ba kowa amma za su yi fice kafin ƙarshen shekara,” in ji shi.

 

A bangaren kasa da kasa, Adeboye ya ce za a samu shiga tsakani na Allah a sassan duniya da abubuwa suka yi zafi a halin yanzu. Bugu da ƙari, za a sami ci gaba mai girma a matakin duniya wajen gano magungunan cututtuka kamar ciwon daji, asma, hauhawar jini, ciwon sukari, da sauransu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending