Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu nan take

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu nan take.

Advertisement

 

Kakakin shugaban Najeriyar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da matakin dakatar da ministar jinkan ta cikin wata sanarwa da aka fitar a yau.

Advertisement

 

Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin ba da dama ga hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike a kanta.

Advertisement

 

Tun farko al’ummar Najeriya sun yi ta matsin lamba akan sai an Dakar da ita inda suke kiraye-kiraye GA gwamnatin tarayya data dakatar da ita daga mukaminta domin a gudanar da cikakken bincike a kanta game da zarge-zargen da ake mata.

Advertisement

 

Ana zargin ta da bayar da umarnin tura kuɗi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun bankin wata mata kamar yanda kafafen yada labarai da dama suka rawaito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending