News
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Ƴan Najeriya Da Su Daina Tarawa Ƴan Bindiga Kuɗi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A jiya Laraba ne gwamnatin tarayya ta gargadi ƴan Najeriya game da yadda jama’a ke rige-rigen tara kuɗi domin biyan kudin fansa ga wadanda aka yi garkuwa da su, inda ta ce hakan zai ƙara ƙaimi wajen satar mutane.
Ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar shi ne ya yi wannan gargaɗin a lokacin da yake ansa tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan gudanar da taron majalisar ministocin tarayya na farko na shekarar 2024 wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a zauren majalisar da ke fadar shugaban ƙasa, a Abuja.
Ministan Ya ba da wannan shawarar ne biyo bayan rahotannin da ke yawo inda aka ji ƴan Najeriya sun tara sama da Naira miliyan 50 domin biyan kudin fansa dan a sako sauran ‘ya’yan Al-Kadriya mata biyar da aka sace.
Ministan ya kara da cewa yayin da gwamnati ta yi matukar damuwa da satar mutane, biyan kuɗin fansa da mutane ke yi hakan zai ƙara dagula shirin Gwamnati
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
