Connect with us

News

Kotu Ta Soke Kasafin Kudin Jihar Ribas Na Naira Biliyan 800

Published

on

 

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na Naira biliyan 800 na shekarar 2024 da Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar.

Advertisement

Da yake yanke hukunci a safiyar Litinin, Mai Shari’a James Omotoso ya ce kasafin da gwamnan ya gabatar a gaban mambobi hudu na majalisar da ke tsaginsa, haramtacce ne.

Babu Jariri Da Aka Sace A Asibitin Waziri Shehu Gidado Karkashin Kulawar mu  – DR Nagoda

Don haka ya umarci gwamnan ya sake gabatar da kasafin a gaban halastaccen zauren majalisar karkashin jagorancin Martin Amaewhule, daga tsagin tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Advertisement

Rikicin Wike da Fubara ya raba kan majalisar dokokin jihar, inda akasarin mambobin suke bangaren Wike suka kuma sauya sheka zuwa APC, har suka tsige sohon shugaban majalisar suka nada daya daga cikinsu.

Gwamnan ya rike kudaden majalisar sannan ya sauya wa magatakardan majalisan da mataimakinsa wurin aiki, a matsayin martinsa kan baren ’yan bangaren Wike.

Advertisement

Amma alkalin ya sanar cewa gwamnan ba shi da hurumin hana majalisar dokokin jihar kudadenta.

Daga nan ya yi wa gwamnan gargadi game da yunkurin kawo cikas ko yin katsalandan ga harkokin gudanar da majalisar da Amaewhule ke jagoranta.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa Alkalin ya kuma soke sauyin wurin aiki da gwamnan ya yi wa magatakardan majalisan da mataimakinsa.

Haka zalika ya umarci Sufeto-Janar na yan Sandan Najeriya ya ba da isasshen tsaro ga shugaban majalisar da mambobin majalisar da ke adawa da gwamnan.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending