Connect with us

News

Hukumar NJC Ta Dakatar Da Alkalan Manyan Kotuna A Jahohi 2

Published

on

NJC Ta Dakatar Da Alkalan Manyan Kotuna A Anambra Da Ribas

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Majalisar kula da harkokin shari’a ta Najeriya (NJC) ta dakatar da Mai Shari’a G.C Aguma na babbar kotun jihar Ribas da Mai Shari’a A.O Nwabunike na babbar kotun jihar Anambra daga gudanar da harkokin shari’a.

Advertisement

An dakatar da alkalan 2 ne tsawon shekara guda ba tare da albashi ba sannan za’a cigaba da sanya idanu a kansu tsawon shekaru 2 a nan gaba.

Za’ A Dauki Tsawan Lokaci Kafin A Gama Gyaran Matsalar Wutar Lantarki A Arewacin Najeriya – Rahoto

A cewar sanarwar da NJC din ta fitar a yau Juma’a, an dauki wannan mataki ne yayin karo na 107 na taron majalisar da babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta jagoranta tsakanin ranakun 13 da 14 ga watan Nuwambar da muke ciki.

Advertisement

Jumlar alkalai 5 aka hukunta saboda aikata laifuffuka daban-daban.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa majalisar ta bada shawarar yiwa wasu alkalan 2 ritayar dole saboda shigar da bayanan karya game da shekarunsu na haihuwa.

Advertisement

An bada shawarar yiwa alkalan 2 da suka hada alkalin alkalan jihar Imo, Mai Shari’a T.E Chukwuemeka Chikeka da girandi kadin jihar Yobe, Kadi Babagana Mahdi, ritayar dole saboda samunsu da yin karya game da shekarunsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending