News
Babu Jariri Da Aka Sace A Asibitin Waziri Shehu Gidado Karkashin Kulawar mu – DR Nagoda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kula da asibitocin jihar Kano sun karyata labarin da ke cewa an sace wani jariri da aka haifa a babban asibitin Waziri Shehu Gidado a karkashin kulawar asibitin.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’ar yada labarai ta hukumar Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda Ranka
Sanarwar ta ce Mahaifiyar jaririn ta zo ne tare da jaririn da kakarsa a matsayin mai kula da mara lafiya wanda ke da alhakin kula da jaririn.
A ranar Juma’a 19 ga watan Junairun 2024 kakar yaron tana rike da yaron a unguwar ta yanke shawarar zuwa yin sallah inda wata baiwar Allah da ke zaune a gefenta ta mika mata yaron.
Bayan ta idar da sallah sai kakar ta zo daukar jaririn wanda a lokacin ne ta lura ba matar a inda ta barta.
An sace jaririn da ake magana a kai daga wurin a tsakanin karfe 6:30 zuwa 7:30 na yamma.
A dai-dai wannan lokacin ne kakar ta yi wata sanarwa wadda ta jawo hankalin daukacin mahukunta da ma’aikatan cibiyar da ke bakin aiki kuma nan take suka fara bincike ko za su iya gano matar.
Wurin dai wani katafaren gida ne wanda ke ganin majinyata sama da 300 a rana, wasu kuma suna da jarirai da ke shigowa a matsayin marasa lafiya ko kuma ‘yan uwan marasa lafiya.
Yana da matukar muhimmanci a fahimci cewa wannan sakaci ne daga bangaren mai kulawa ba asibiti ba.
Asibitin ya shiga tsakani wajen neman yaron da ya bace a matsayin wani bangare na aikin da ya rataya a wuyansa na taimakon iyayen da ba su da komai da kuma yadda aka sace jaririn
a wurin.
