News
Dr. Labaran Ya Tabbatar wa Kungiyar Lafiya Programme Ci Gaba da Aiki da Ita
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Kwamishinan lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Yusuf, ya jaddada aniyar ma’aikatarsa ta ci gaba da gudanar da huldar aiki tare da Kungiyar Lafiya Programme domin ci gaban fannin lafiya a jihar.
Dakta Labaran ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar ta kasa da ta kai masa ziyara a ofishinsa.
Aljeriya Ta Kori Kocinta Bayan Cire Ta A Gasar Cin Kofin Afrika.
Kwamishinan ya nuna jin dadinsa da cewa Alhaji Abba Kabir ya tabbatar da kansa a matsayin Gwamna mai son fannin lafiya, wanda yake yin iyakar iyawarsa ba tare da gajiyawa ba wajen inganta harkar kiwon lafiya a jihar zuwa matakin da ya dace.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka.
Kwamishinan ya kara da cewa, a cikin ‘yan watanni da gwamnatin ta yi, Gwamnan ya dauki likitoci 107 aiki a matsayin matakin gaggawa domin dakile matsalar karancin ma’aikata a bangaren kiwon lafiya da aka rarraba su asibitoci daban-daban a fadin jihar domin inganta aiki.
Ya kuma ce, an umurci hukumar kula da manyan asibitoci da takwararta ta lafiya a matakin farko da su yi bincike a asibitocin da ke karkashinsu don gano gibin ma’aikatan da suke da su, da kuma adadin ma’aikatan da ake bukata domin cike gibin domin mika wa mai girma Gwamna domin neman sahalewarsa a ɗaukar ƙari.
Dakta Labaran ya bayyana cewa yana aiki tare da babban jami’in kididdiga na jihar domin samun cikakken tsarin adana bayanai na jihar, ya kara da cewa ya kuma ba da shawarar a ware jami’i a ma’aikatar wanda zai rika tattara bayanan da ofishin kididdiga ke bukata.
Ya sanar musu cewa, a kwanakin baya ne Gwamnan ya amince da samar da wani sabon shiri mai taken ABBA CARE, wanda zai dauki masu ciwon sikila 39,000 a lokuta daban-daban, inda za a fara da marasa lafiya 56 da suka hada da mata masu juna biyu da tsofaffi da kuma sauran masu rauni.
Ya gode wa Kungiyar Lafiya Programme bisa irin gudummawar da suke bai wa jihar tsawon shekaru wajen daidaita fannin kiwon lafiya na jihar da nufin ganin an samu tagomashi a duniya, yana mai ba su tabbacin ci gaba da gudanar da aiki tare cikin fahimtar juna domin cimma manufofin da aka sa gaba.
Tun da farko, Shugaban Kungiyar Shirin Lafiya n Kasa, Dakta Usman Gwarzo, ya yi ce sun je ma’aikatar ne domin tattauna batutuwan da suke da alaka da hadin gwiwar da suka fara da gwamnatin jihar, tare da karfafa goyon bayansu musamman ga wannan sabon ci gaban da aka samu na hukuncin da kotu ta yanke wanda ya daidaita tafiyar gwamnati.
Ya jaddada cewa Kano na daya daga cikin jihohi masu muhimmanci na FCDO, wanda ke samar wa Shirin Lafiya kudade da jihohin Jigawa, Kano da Kaduna a matsayin jihohin da suke sahun gaba, inda Kano ta fi sauran nuna himma wajen karfafa tsarin kiwon lafiya kamar yadda ya kamata ta yadda ta kasance jiha ta farko a kasar da ta kafa hukumar dakile cututtuka wadda suka taka rawar gani wajen ganin ta samu tabbata.
Dakta Gwarzo ya bayyana cewa, sun kuma tallafa wa gwamnatin jihar Kano a fannonin da suka shafi lafiyar mata masu juna biyu, haihuwa da jarirai sabbin haihuwa, samar da kudade don yin tsare-tsare a fannin kiwon lafiya ta hanyar shirin taimakekeniyar lafiya, yana mai tabbatar da cewa mafi yawan ayyukan suna yin ne don karfafa kiwon lafiya matakin farko ta hanyar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko.
Ya kuma tabbatar wa Kwamishinan kudirinsu na tallafa wa jihar wajen kafa sashin kula da lafiyar iyali domin samun damar hada dukkan harkokin kiwon lafiyar haihuwa da kuma marawa jihar baya wajen fadada komarta ta samar da tsaron fannin lafiya a lokaci guda kuma da samar da kudaden tafiyar da harkokin kiwon lafiya da suka hada da daukar ma’aikata.
