Connect with us

News

Mun Fara Ziyarar Aiki Ba Tare Da Bata Lokaci Ba Dan Tsaftace Harkar Lafiya A Jihar Kano — Dr Nagoda

Published

on

Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

 

Advertisement

Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Dakta Mansur Mudi Nagoda da tawagarsa, sun fara gudanar da ziyarar aiki ba tare da bata lokaci ba a duk wani cibiyoyi da ke karkashin kulawar hukumar a wani bangare na kokarin tsaftace harkar lafiya a jihar.

A bisa bin umarnin shugaban ma’aikatan da tsara ziyarce-ziyarcen da mai girma kwamishinan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf, da manyan sakatarorin gwamnati da manyan daraktocin hukumomin lafiya na jihar za su gudanar.

Advertisement

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, Ya Mayar Da Martani Akan Gayyatar Da Ganduje Ya Yi Masa Na Neman Shiga Jam’iyyar APC

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami ar yada labarai ta hukumar Samira Suleiman ta turawa da Jaridar Inda Ranka 

Sanarwar ta kara da cewa Dokta Nagoda ya bayyana cewa masu sa ido za su kai ziyarar bazata zuwa dukkan shiyyoyin da aka ware musu ta hanyar amfani da tsarin kulawa don duba wurin.

Advertisement

Haka kuma Lambobin tarho da ofisoshin Servicom, Tsaftar muhalli, Tattaunawa da marasa lafiya kan gamsuwarsu da ayyukan da aka yi musu za su kasance cikin tantancewar.

Ya kamata a lura cewa hukumar tana da ikon ɗaukar matakin gaggawa da kuma ba da tambaya idan hakan ta kama.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa Dr Nagoda ya yi gargadi ga daukacin ma’aikatan lafiya kan al’amuran da suka shafi aiki a dukkanin cibiyoyin da suka hada da rashin zuwa aiki, gujewa aiki, kyamar mara lafiya da dai sauransu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending