Connect with us

News

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum uku kan zargin satar awaki 48

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum uku kan zargin satar awaki 48 a Kananan Hukumomin Babura da Kiyawa na jihar.

Advertisement

Kwamishinan na yan sandan jihar, Ahmadu Abdullahi ne, ya shaida wa manema labarai a Dutse a ranar Alhamis.

Mun Fara Ziyarar Aiki Ba Tare Da Bata Lokaci Ba Dan Tsaftace Harkar Lafiya A Jihar Kano — Dr Nagoda

Ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne, a wani samame daban-daban tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

Advertisement

Abdullahi, ya ce, biyu daga cikin su ana zargin su da hada baki da wani mutum wajen sace awaki 26, wanda kudin su ya kai Naira miliyan 1.3.

Aminiya ta ruwaito cewa wani mutum mai suna Hassan Ibrahim ne, daga kauyen Abari a Jamhuriyar Nijar, ya shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na Babura a ranar 22 ga watan Janairu, cewar an sace masa awaki da kundinsu ya kai Naira miliyan 1.3.

Advertisement

Ya ce rundunar, ta samu wasu bayanai lokacin da ta fara bincike, lamarin da ha kai ga cafke wani mutum da awaki takwas.

Kwamishinan, ya ce wadanda ake zargin bayan shiga hannu sun amsa laifin satar awaki 26.

Advertisement

Ya kara da cewa mutum na uku da ake zargi wanda mazaunin kauyen Dundubus ne a Dutse, an kama shi da awaki 22 da ake zargin na sata ne.

Kazalika, Kwamishinan ya ce za a gurfanar da su a kotu da zarar sun kammala bincike a kan su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending