Connect with us

News

Kamata yayi a dinga baiwa Yan sandan Nigeria 250 mafi Karancin albashi

Published

on

Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya Olukayode Adeolu Egbetokun

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

Ganin yadda matsalar tsaro ke ci gaba da ta’azzara a Najeriya da kuma yadda rayuwa tayi tsada, wani masanin harkar tsaro Mathew Ibadin ya bukaci hukumomin Najeriya da su sanya kudin da ya kai naira dubu 250 a matsayin albashi mafi karanci ga jami’an ‘Yan sandan kasar.

Advertisement

 

 

Advertisement

Ibadin wanda ya kuma bukaci gwamnati ta amince wajen bada lasisi ga masu bincike dake zaman kansu, kamar yadda ake samu a kasashen da suka ci gaba, yace karin albashin zai kara kaimi ga jami’an dake aiki da rage cin hanci da rashawa da kuma bai wa kwararru a fannoni daban daban damar shiga aikin domin inganta shi.

Masanin harkar tsaron ya kuma bukaci bai wa fitattun mutanen da aka amince da sahihancin su lasisin mallakar bindiga domin kare kan su daga barazanar tsaron da ake fuskanta, ganin yadda ayyukan masu garkuwa da mutane ke dada fadada a cikin kasar.

Advertisement

Daga cikin irin wadannan mutane, jami’in yace akwai sarakunan gargajiya da manyan jami’an gwamnati da malaman makarantu da shugabannin kamfanoni da makamantan su.

Ibadin ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ya dace gwamnati ta kafa wata hukuma da zata dinga kula da shirin bada lasisin mallakar makaman ga jama’a domin tabbatar da cewar irin wadannan makamai da ake magana basu fada hannun bata gari ba.

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending