News
Hukumar ‘yan sanda ta kama jami’an ta da suka yi wa mutum biyu fashi da makamin Dala 3,000
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas ta ƙaryata zargin cewa ta saki jami’an ta uku da ta kama sun yi fashin Dala 3,000 a hannun wasu ‘yan Najeriya.
An dai yi zargin cewa bayan ta kama su ta gabatar da su ga manema labarai, daga baya an sake su, sun ci gaba da yawon su, ba tare da an gabatar da su kotu ba.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ribas, Grace Iringke-Koko ce ta yi bayanin cewa ba a sake su ba, kamar yadda wasu ke zargi.
Grace ta yi bayani a shafin ‘yan sanda na X a ranar Juma’a.
Ta na magana ne a matsayin raddi kan zargin da wani lauya daga Jihar Delta, mai suna Harrison Gwamnishu ya wallafa a wani shafin sa na sada zumunta a soshiyal midiya, inda ya yi zargin cewa an saki masu laifin su na yawon su.
Ya ce wasu mutanan sun gan su ma su na yawo cikin gari.
Kakakin ta ce “wanda ya ce an gan su suna yawo a gari ƙarya ya ke yi, sharri ne da kuma ƙage ne.” Ta bayyana haka.
Ta ce an kulle jami’an ‘yan sandan a sashen CID, kuma ana kan yi masu irin horon da ya dace a yi wa kowane ɗan sandan da aka samu da irin laifuka ko laifin irin wanda suka aikata.
“Mu na kira ga jama’a su yi biris da ƙarairayin da ake yaɗawa cewa an saki ‘yan sandan su na yawo. Saboda za mu kawo bayanan halin da kwamitin ladaftarwa ke ciki.”
Su dai ‘yan sandan uku cikin watan jiya ne sun baro Jihar Ribas za su tafi Jihar Abiya, su ka saci mutum biyu su ka nausa Jihar Delta da su, daga can suka nausa Jihar Bayelsa da su, sannan su ka zube su a Fatakwal, Jihar Ribas, bayan sun ƙwace Dala 3,000 a hannun su.
Daga baya dai an gano kuɗaɗen a hannun ‘yan sandan, kuma aka maida kuɗaɗen ga masu su.
