News
An Ceto Yarinyar Da Aka Sayar N100,000 A Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An ceto wata yarinya ’yar shekara shida wadda aka sace aka kuma sayar da ita N100,000 a Jihar Kaduna.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce bayan samun rahoton bacewar yarinyar ranar 23 ga Janairu, jami’anta suka sunkuya bincike wanda a karshe aka kama wata makwabciya da ake zargi da hannu a bacewar ’yar.
“A halin bincike an sake kama wani mutum da wata mata da suke da hannu a bacewar yarinyar,” in ji rundunar.
Ta kara da cewa an kubutar da yarinyar ce ba tare da wani rauni ba bayan kuma an sayar da ita a kan N100,000.
Aminiya ta rawaito cewaTuni dai aka sake hada yarinyar d a iyayenta.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
